Shugaba Buhari ya hakikance a kan batun yin ram da barayin Najeriya

Shugaba Buhari ya hakikance a kan batun yin ram da barayin Najeriya

Mun ji cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya kara jaddada aniyar sa na yaki da rashin gaskiya a Kasar nan a sakon barka da sallar da aikawa Musulman Najeriya a lokacin hutun nan.

Shugaba Buhari ya hakikance a kan batun yin ram da barayin Najeriya
Buhari tare da Hadiman sa a Daura. Hoto daga: Bashir Ahmaad

Shugaba Muhammadu Buhari yayi amfani da shafin sa na kafar sada zumunta na Tuwita inda yayi kira ga ‘Yan kasar nan su daina hadama da zari da kuma satar dukiyar kasa. Shugaba Buhari dai ya nemi jama’a su zama masu gaskiya.

Kamar yadda mu ka samu labari, Shugaban kasar yayi amfani da wannan lokaci da Sallar babban Idi inda yayi kira ga jama’a su hada kai da kaunar juna. Shugaban ya kuma kara bayyana cewa dole ayi maganin rashin gaskiya a Najeriya.

KU KARANTA: Gwamna Nasir El-Rufai yayi sallah a kudancin Kaduna

Mai magana da yawun bakin Jam’iyyar APC Yekini Nabena yayi irin wannan kira inda ya nemi jama’a su hada kai tare da marawa Shugaba Buhari ya cika alkawarin da ya dauka. APC tace a haka ne kurum kasar nan za ta kai ga ci.

Jam’iyyar APC tayi kira a wannan lokaci ta bakin Sakataren yada labaran ga xmutane cewa su hada kai tare da ganin girma da darajar kowa. APC tace Ubangiji ya hallici mutane dabam-dabam ne domin a fahimci juna a kuma zauna lafiya.

Dazu kun ji labari cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki yana Jihar Kwara inda yake hutun sallah tare da jama’ar sa. Dama can kun ji labari cewa Wazirin na Ilorin ya bada gudumuwar kudi domin ayi bikin hawan sallah a Jihar Kwara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel