Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe

Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe

- Bayan wata musayar wuta, Sojoji sun hallaka 'yan bindiga da dama

- Nasarar jami'an Sojojin dai ta zo ne da agajin taimakon jirgin sama na yaki

- Duk da wasu daga cikin 'yan bindigar sun tsere da raunuka, Sojojin na sake shirin binsu don gamawa da su

Babban kwamandan atisayen Whirl Stroke Manjo janar Adeyemi Yekini (OPWS) ya tabbatar da nasarar rundunar na bindige wasu ‘yan bindigar da suke dauke da makamai har su goma a yankin Gbajimba-Akor-Tomata dake karamar hukumar Guma ya jihar Benuwe.

Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe
Sojoji sunyi sukuwar Sallah kansu wasu 'yan bindiga a jihar Benuwe

Kwamandan ya kuma tabbatar da cewa sunyi rashin Soja guda yayin artabun a ranar Asabar, sannan biyu kuma sun samu raunuka.

Da yake shaidawa manema labarai a garin Makurdi, Manjo Yakini ya shaida cewa basu san yawan wadanda suka jikkata daga bangaren ‘yan bindigar ba, sakamakon agaji da jirgin saman Mi35 ya kawo musu ta hanyar yin barin wuta ga ‘yan bindigar da suke kan babura.

KU KARANTA: Cikin EFCC ya duri ruwa, an kai ta kara ana bukatar ta biya diyyar Naira N50b

“Yayin da muke musayar wuta, jirgin Mi35 ya hango ‘yan bindigar kimanin su ashirin haye kan Babura suna shirin tsallakawa jihar Nassarawa.

Nan take harin farko da jirgin ya kai ya gama da 15 daga cikinsu, yayinda da wasu suka tsere da raunuka a jikinsu.

Daga nan ne jami’anmu suka bi su har sai da suka cimmusu a wani yankin mararrabar jihar Nassarawa da Benuwe.

Yanzu haka ana shirye-shiryen bin sahunsu domin tabbatar da karkade su baki daya a jihar.” Yekini ya bayyana.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel