Wani babban ‘Dan APC a Katsina ya sauya sheka zuwa PDP bayan an yi watsi da shi
Babbar Jam’iyyar adawa a Najeriya watau PDP tana kara karfi inda wani babban ‘Dan siyasa a Yankin Funtua ta Jihar Katsina da ke Arewacin Najeriya da Mabiyan sa 10, 000 su ka sauya-sheka kwanan nan bayan sun ga ba ayi da su.

Dazu mu ka samu labari daga Channels TV cewa wani tsohon ‘Dan Majalisar Jihar ta Katsina Shehu Inuwa Imam ya fice daga APC ya koma Jam’iyyar PDP. Shehu Imam yace APC ba tayi masa dare ba duk da kokarin da yayi mata.
Tsohon ‘Dan Majalisar ya wakilci Yankin Faskari/Sabuwa/Kankara a Majalisar Tarayya inda yanzu ya koma PDP domin ba ayi da shi. Shugaban PDP na Jihar Katsina Yusuf Salisu Majigiri yayi alkwarin yi wa ‘Yan siyasar adalci.
KU KARANTA: Wani ya yabawa kokarin Gwamnatin Shugaba Buhari
Alhaji Yusuf Majigiri ya bayyana cewa PDP za tayi nasara a Jihar Katsina inda Shugaba Buhari ya fito. Wadanda su ka halarci taron yi wa manyan ‘Yan siyasar wanka sun hada da Muttaqha Rabe Darma, Abdullahi Faskari, Lado Danmarke
Dama dai asali Honarabul Shehu Imam ‘Dan PDP ne don haka yace ya koma gida. Shehu Inuwa Imam yace APC ba ta ga kokarin da yayi a 2015 ba don haka ya fice. Ana sa rai wasu manyan ‘Yan siyasar Jihar za su bar APC nan gaba kadan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng