Yadda wani Bawan Allah ya zama Matukin jirgi daga aikin goge-goge

Yadda wani Bawan Allah ya zama Matukin jirgi daga aikin goge-goge

Mun samu labarin wani Bawan Allah mai shara a da da yanzu ya zama babban matukin jirgin sama. Kyaftin Muhammad Abubakar ya fara aiki ne a matsayin mai goge amma yanzu likafa tayi nisa.

Yadda wani Bawan Allah ya zama Matukin jirgi daga aikin goge-goge
Kyaftin Mohammed Abubakar ya zama Direba bayan fara da aikin shara

Muhammad Abubakar yayi hira da Jaridar Daily Trust inda ya bada tarihin rayuwar sa. Abubakar ya nemi cigaba da karatu bayan ya kammala Sakandare amma bai dace ba, dalilin haka ya fara aikin goge-gogen jirgi a Kaduna.

Wannan Bawan Allah ya soma ne da aiki da Kamfanin jirgin Kabo a lokacin wani aikin Hajji inda ake biyan sa N200 a kullum. Bayan shekara da shekaru yana aiki ya kuma samu kwarewa har ya koma kamfanin jirgin nan na Aero.

KU KARANTA: An nemi a ga bayan wata fitacciyar Ministar Shugaba Buhari

A kamfanin Aero ne Muhammad Abubakar ya fara samun albashi mai tsokan da ya girgiza sa saboda irin kokarin sa. Muhammad yace a nan aka fara biyan sa N170, 000 a kowane wata don haka ya shiga adana kudin sa yana adashe.

Bayan wannan Bawan Allah ya tara makudan kudi ne ya ruga Kasar Kanada inda yayi kwas kn harkar tukin jirgi, bayan ya dawo gida ne kuma sai ya nemi kudin yin lasisi abin ya faskara don haka kamfanin sa su ka dauki nauyin karatun sa.

Kafin dai ka ce mene sai ga wannan mutumi da ya fara aiki a matsayin mai goge-goge ya zama babban Direban jirgi. Muhammad yayi shekaru 8 da Kamfanin Aero inda yanzu yake kuma aiki da kamfanin nan na Azman Air har ya shekara 2.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel