Shugaban Najeriya ya aikawa Mutanen Ghana da Nane Maria Annan ta’ziyyar Marigayi Kofi Annan

Shugaban Najeriya ya aikawa Mutanen Ghana da Nane Maria Annan ta’ziyyar Marigayi Kofi Annan

Mun samu labari cewa Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari da sauran manyan Shugabannin kasashe na Duniya irin su Faransa, Ingila, Indiya da sauran su sun aika sakon ta’aziyyar su na rasuwar Marigayi Kofi Annan da ya rasu jiya.

Shugaban Najeriya ya aikawa Mutanen Ghana da Nane Maria Annan ta’ziyyar Marigayi Kofi Annan
Buhari ya kira Nana Akufo-Addo game da rasuwar Kofi Annan

Shugabannin Duniya sun nuna alhinin su na rashin tsohon Shugaban Majalisar Dinkin Duniya Kofi Annan wanda ya bar Duniya jiya yana shekara 80. Shugaba Buhari yana cikin wadanda su ka fara yi wa mutane ta’aziyyar wannan rashi.

Shugaban kasa Buhari ya kira Shugaban kasar Ghana Nana Akufo-Addo tun yana Landan inda yayi masa ta’aziyyar wannan babban rashi da Afrika da ma Duniya gaba daya tayi. Shugaban Birtaniya ma dai ta aika ta’aziyyar ta tuni.

KU KARANTA: Buhari yayi waya da wani Gwamnan Kudancin Najeriya bayan rasuwar Mahaifiyar sa

Femi Adesina wanda ke magana da yawun Shugaban Najeriya ya bayyana cewa ba za a manta da kokarin da Kofi Annan yayi musamman wajen ganin an yi yaki da cutar Kanjamau a Duniya ba. Buhari yayi wa Iyalin Marigayin ta’aziyya.

Kofi Annan ya shugabanci Majalisar Dinkin Duniya ne daga 1997 zuwa 2006 lokacin da Ban-Ki Mon ya karba. Ana ji da Annan a Afrika da ma Duniya gaba daya inda har ya karbi kyautar Nobel ta zaman lafiya a Duniya a shekarar 2001.

Mun samu labari cewa Kofi Annan ya fara auren wata ‘Yar Najeriya ne mai suna Titi Alakija a shekarar 1965 kafin su rabu a cikin shekarun 1970. Daga baya ne Annan ya auri ‘Yar Garin su Nane Maria a 1983 wanda ya mutu ya bari a yanzu.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel