2019: Tudun-tsirar da Shugaba Buhari da APC za su tsallake nan gaba

2019: Tudun-tsirar da Shugaba Buhari da APC za su tsallake nan gaba

Jiya ne Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya dawo gida Najeriya bayan ya dauki wani lokaci yana shakatawa a Ingila. Daily Trust ta zayyano wasu aikin da ke gaban Shugaba Buhari kafin zabe mai zuwa ganin yadda zaben ya karaso.

2019: Tudun-tsirar da Shugaba Buhari da APC za su tsallake nan gaba
Shugaba Buhari da APC za su gamu da wasu matsaloli game da 2019

1. Atiku da sauran ‘Yan takara

Daga cikin matsalolin da Shugaba Buhari zai fuskanta shi ne kalubale a Arewacin Kasar nan domin kuwa akwai manyan ‘Yan takara irin su Tsohon Mataimakin Shugaban kasa Atiku Abubakar da za su nemi kujerar Shugaban kasa a PDP.

2. Masu sauya-shekar siyasa

Bayan nan kuma dai akwai wasu manya a Jam’iyyar APC da su ka sauya sheka su ka koma Jam’iyyun adawa, idan dai ba a manta ba hakan yana cikin irin abubuwan da su ka kai tsohon Shugaban kasa Jonathan ya fadi zabe a 2015.

KU KARANTA: Abin da ya sa Sanata Kwankwaso ya bar APC ya koma PDP

3. Matsalar tsaro a kasa

Masana harkar siyasa sun bayyana cewa zai yi wahala Jihohin Arewa maso tsakiya su bi bayan APC a 2015. Jihohin dai sun zabi Buhari ne saboda alkawuran da yayi a baya sai dai matsalar tsaro ta afka masu bayan Shugabari ya lashe zabe.

4. Rashin goyon baya daga wajen Inyamurai

Shugaba Buhari dai bai taba yin nasara a Kudu maso Kudanci da kuma Kudu maso Gabashin kasar ba don haka wannan karo zai so ya samu kuri’u a Yankin. Sai dai da wuya Inyamurai su mara masa baya saboda su na ganin an ware su a Gwamnatin APC.

Kun san cewa Buhari yayi hira da ‘Yan jarida bayan ya dawo Najeriya jiya kuma daga cikin abin da Shugaba Buhari ya fada shi ne za su kama barayin Najeriya wadanda su ka saci kudi su ka kuma kashe tattalin arzikin kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel