Ya kamata a sake duba lamarin Almajiranci a Najeriya – Ribadu

Ya kamata a sake duba lamarin Almajiranci a Najeriya – Ribadu

Tsohon Shugaban Hukumar EFCC Nuhu Ribadu ya nemi ayi gyara game da yadda ake gudanar da harkar karatun Almajiranci a Arewacin Najeriya. Ribadu yayi wannan bayani ne a wajen wani taro da Jaridar Premium Times ta shirya.

Ya kamata a sake duba lamarin Almajiranci a Najeriya – Ribadu
Nuhu Ribadu yace an bar Arewa a baya a Duniya

Malam Nuhu Ribdu ya bayyana cewa mafi da-dama ana cin zarafin Almajirai a Kasar saboda halin da su ka samu kan su. Ribadu ya kuma bayyana cewa mafi yawan lokaci, Almajirai su na cikin wadanda rikicin addini ke rutsawa da su.

Ribadu da yake jawabi ya bayyana cewa yana cikin wadanda su kayi bincike game da rikicin da aka yi shekarun baya a Kaduna, Ribadu yace mafi yawan wadanda aka kashe a rikicin kananan yara ne da su ka shigo Gari neman karatu.

KU KARANTA: An gudanar da kidayar awaki a wata Kasar Afrika

Tsohon Shugaban na EFCC yace Arewacin Najeriya ne ci-ma-baya a kaf Duniya a yanzu ya kuma kara da cewa irin wannan bara da ake yi bai dace ba. Ribadu wanda ya fito daga Yola yace matsalar Almajiranci ta dabaibaye Arewacin kasar nan.

A wannan tsari da ake tafiya dole a sakewa Almajiranci zane idan ha rana so a cigaba a Kasar inji Nuhu Ribadu wanda yayi takarar Shugaban kasa da Gwamna amma bai kai labari ba in ji Jaridar Premium Times

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel