Babban Sallah: Kakakin majalisar Oyo ya bukaci Musulmai da suyi adu’a domin yin zabe cikin lumana a 2019

Babban Sallah: Kakakin majalisar Oyo ya bukaci Musulmai da suyi adu’a domin yin zabe cikin lumana a 2019

Yan kwanaki kafin bikin babban Sallah, kakakin majalisar dokokin jihar Oyo, Olagunju Ojo ya bukaci Musulmai, musamman mahajattan Najeriya dake kasa mai tsariki da suyi addu’an samun nasara ga zaben 2019.

Ojo ya bada wannan shawara ne a sakonsa na Eid-el-Kabir da ke gabatowa ta hannun hadiminsa na musaman a kafofin watsa labara, Mista Yemi Alao a ranar Juma’a a garin Ibadan, babban birnin jihar Oyo.

Babban Sallah: Kakakin majalisar Oyo ya bukaci Musulmai da suyi adu’a domin yin zabe cikin lumana a 2019
Babban Sallah: Kakakin majalisar Oyo ya bukaci Musulmai da suyi adu’a domin yin zabe cikin lumana a 2019

Ya kuma yi kira ga Musulmai da su nemi zabin Allah da yafiyarsa kan jihar da shugabanninta yayinda suke kula da lamuran jihar.

KU KARANTA KUMA: Daruruwan mutane sun yi gangami a Jigawa domin marawa sanatan da ya koma PDP baya

Ya kuma ba al’uman jihar tabbacin cewa za su ci gaba da jajircewa don ganin sun daukaka martabar jihar da mutanenta.

A baya Legit.ng ta rahoto cewa gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranakun 21 da 22 ga watan Agusta a matsayin hutun bikin babban Sallah.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel