Mugunta iya mugunta: Matasa 3 sun murɗe wuyan wani tsoho mai shekaru 105 har lahira

Mugunta iya mugunta: Matasa 3 sun murɗe wuyan wani tsoho mai shekaru 105 har lahira

Rundunar Yansandan jihar Enugu ta sanar da kama wasu matasa guda uku da take zargi suna da hannu cikin kashe wani tsoho mai shekaru dari da biyar (105) a rayuwa, Cif Eze Nwah-Onuh a karamar hukumar Igboeze ta Arewa na jihar Enugu.

Kamfanin dillancin labaru, NAN, ta ruwaito Kaakakin rundunar Yansandan jihar Enuu, SP Ebere Amaraizu ne ta sanar da haka cikin wata sanarwar da ta fitar a ranar Juma’a, 17 ga watan Agusta.

KU KARANTA: Buhari da Ganduje zasu samar da bahaya miliyan 20 a jihar Kano

Kaakaki Ebere ta bayyana sunayen masu laifin kamar haka; Onyeka Abugu mai shekaru 22, Ogbonna Eze mai shekara 22 da Nnamdi Eze mai shekaru 19, inda tace a yanzu haka suna baiwa rundunar hadin kan da ya dace.

Ebere tace a ranar 9 ga watan Agusta ne matasan suna shake wutar Nwa-Onu a kauyensa dake Ekposhi Umidoko, har sai da yace ga garinku nan, kuma tuni aka jibge gawarsa a dakin ajiyan gawarwaki na Asibitin garin.

Duk da cewa Kaakakin tace basu dan dalilin da yasa matasan suka kashe Nwa-Onu ba, amma kwararrun jami’an Yansandan farin kaya zasu cigaba da gudanar da bincike game da lamarin.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags:
Online view pixel