Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis

Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis

- Fitacciyar 'yar wasan kwallon tennis dinnan Serena Williams ta bayyana cewa ta samu rashin nasara ne wanda ya fi kowanne girma a tarihin rayuwar ta

- Johanna Konta ita ce ta doke Serena a zagaye na farko a wasan da suka buga a San Jose a watan Yulin da ya gabata

Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis
Kuji dalilin da ya hana Serena Williams cin wasa kwallon tennis

Fitacciyar 'yar wasan kwallon tennis dinnan Serena Williams ta bayyana cewa ta samu rashin nasara ne wanda ya fi kowanne girma a tarihin rayuwar ta, tunda ta fara buga wasa, hakan kuma ya farune jim kadan bayan an bata labarin cewa an saki wanda ya kashe 'yar uwarta daga gidan kurkuku.

DUBA WANNAN: Wata yarinya ta kuduri aniyar kare hakkin Fulani

Johanna Konta ita ce ta doke Serena a zagaye na farko a wasan da suka buga a San Jose a watan Yulin da ya gabata.

Robert Edward Maxfield shine wanda ya kashe 'yar uwar ta Serena mai suna Yetunde Price, an sako shine bayan da aka yi masa afuwa, bayan ya shafe shekaru goma sha biyu a gidan kaso bisa kama shi da laifin harbe Yetunde.

Serena ta bayyana cewa ta kasa cire labarin sako Robert daga ranta a lokacin da suke buga wasan da Johanna.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel