Ku daina mafarki da rana tsaka, ba ku isa ku tsige Saraki ba – Jigon PDP ga APC

Ku daina mafarki da rana tsaka, ba ku isa ku tsige Saraki ba – Jigon PDP ga APC

An gargadi shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomole, da ya daina tunanin cewa APC na iya tsige shugaban majalisar dattawa, Dr Bukola Saraki.

Wani jigon jam’iyyar People’s Democratic Party (PDP), jihar Delta, Cif Sunny Onuesoke, a ranar Alhamis, 16 ga watan Agusta ya bayyana hakan a wata sanarwa a garin Warri.

Idan zaku tuna, Oshiomhole yace APC zata bi duk hanyar da ya dace domin tabbatar da cewar ta tsige Bukola Saraki daga matsayin shugaban majalisar dattawa wannan tam aye gurbinsa da wani dan majalisa mai amana.

Ku daina mafarki da rana tsaka, ba ku isa ku tsige Saraki ba – Jigon PDP ga APC
Ku daina mafarki da rana tsaka, ba ku isa ku tsige Saraki ba – Jigon PDP ga APC

Amma Onuesoke, tsohon dan takarar gwamna a jam’iyyar PDP a zaben 2007, yace koda ace dukkanin jihohi 36 na kasar APC ce ke rike da ita, basu da abun da ya kai da zasu tsige Saraki.

KU KARANTA KUMA: An nada jarumi Ali Nuhu jakadan yaki da shan miyagun kwayoyi

Ya shawarci Oshiomhole da ya kyale majalisar dokokin kasar ya mayar da hankali wajen kula da shugabancin jam’iyyarsa.

Yace sanatoci ne kadai ke da damar kawo chanji a majalisar masu rinjaye.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Online view pixel