Wani malamin addini ya musuluntar da aljani a kasar Saudiyya

Wani malamin addini ya musuluntar da aljani a kasar Saudiyya

Wani fitaccen malamin islama dake da'awar tarin ilimi musamman ma a fannin fitar da aljannu watau 'Ruqya' ya ce ya samu nasarar musuluntar da wani gangararren aljani a kasar Saudiyya.

Shi dai malamin addinin da ake kra da Sheikh ya bayyana hakan ne a shafin sa na dandalin sada zumunta na Twitter inda kuma yace aljanin ne da kan sa ya nemi ya musulunta din biyo bayan yadda yaji yana rera ayoyin alqur'ani.

Wani malamin addini ya musuluntar da aljani a kasar Saudiyya
Wani malamin addini ya musuluntar da aljani a kasar Saudiyya

KU KARANTA: Zainab Indomie ta dawo fim gadan-gadan

Legit.ng ta samu cewa jama'a da dama dai sun yi ta tofa albarkancin bakin su game da lamarin inda wasu ke ganin cewa malamin ya shirga karya ne kawai saboda yana son ayi ta maganar sa.

A wani labarin kuma, Mahukunta a kasar Saudiyya sun sanar da cafke wasu masoya da aka gani suna sumbantar junan su a cikin wani faifan bidiyo a wani yanayi mai kama da fasikanci da badala.

Yanzu haka dai masoyan suna fuskantar tuhumar badala da fasikanci tare da shan kayen ma a bainar jama'a wanda hakan ya sabawa dokokin kasar.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel