Ban je ko ina ba; Ina nan a APC daram-dam-dam – James Barka

Ban je ko ina ba; Ina nan a APC daram-dam-dam – James Barka

Mun samu labari cewa Ambasada James Barka wanda ya taba zama Gwamna na rikon kwarya a Jihar Adamawa ya karyata rade-radin cewa ya fice daga Jam’iyyar APC ya koma Jam'iyyar PDP mai adawa da ya bari a 2014.

Ban je ko ina ba; Ina nan a APC daram-dam-dam – James Barka

Barka yace Shugaban PDP a Adamawa ya nemi ya bar APC amma yace yana tare da Buhari

James Barka wanda yana cikin manya a Gwamnatin nan mai-ci, ya bayyana cewa yana nan a APC har gobe. Barka ya bayyana wannan ne lokacin da ya zanta da ‘Yan jarida jiya Laraba a babban Birnin Tarayya Abuja.

Tsohon Mukaddashin Gwamnan ya zargi kafofin yada labarai na zamani da yada labarin cewa ya koma PDP. Ambasada James Barka yace wannan maganar babu gaskiya a cikin ta domin ba ya ko haufin barin Jam’iyyar APC.

KU KARANTA: Wasu Gwamnoni sun ji tausayib Ma'aikata sun biya albashi

Barka, wanda yanzu yana cikin Gwamnatin da Shugaba Buhari ya kafa domin tada Yankin Arewa maso Gabas da ‘Yan Boko Haram su ka yi ta’adi yace yana nan a Jam’iyyar APC mai mulki domin aiki tare da Shugaba Buhari.

Ambasada Barka yace yayi amanna da tafiyar Buhari don haka ba ya kokwanton komawa PDP. Barka yace idan har ya na tunanin barin APC lallai ya cika babban mahaukaci. Yace an yi kokarin ya ganin koma PDP amma ya ki.

Tsohon Jakadan kasar yace ba ya zauna a APC bane saboda mukamin sa, yace yana Jam’iyyar ne saboda gyaran kasar da Shugaba Buhari yake yi. Barka yace a 2014 ya ajiye mukamin Jakada ya dawo gida ya shiga tafiyar APC.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel