Sallah: Gwamna Ahmed yayi umurnin biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Sallah: Gwamna Ahmed yayi umurnin biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Gabannin bikin babban Sallah, Gwamna Abdulfatah Ahmed na Kwara ya umurci ma’aikatar kudi da ta fara biyan albashin ma’aikata na watan Agusta ba tare da bata lokaci ba.

Kwamishinan kudi, Alhaji Demola Banu, wadda ya bayyana hakan a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta a Ilorin yace an kammala shirye-shirye domin ganin ma’aikata sun fara karban albashi daga ranar Alhamis.

Sallah: Gwamna Ahmed yayi umurnin biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Sallah: Gwamna Ahmed yayi umurnin biyan albashin ma’aikata na watan Agusta

Yace gwamnan yayi hakan ne domin tabbatar da cewa ma’aikata sunyi bikin Sallah cikin farin ciki.

KU KARANTA KUMA: Farin jini: Masu shaguna a Saudiyya na amfani da hoto da sunan Buhari domin samun kasuwa

A wani lamari makamanci haka, Legit.ng ta rahoto cewa Gwamna Aminu Tambuwal na jihar Sokoto ya umurci ma’aikar kudi da ta gaggauta fara biyan al’bashin ma’aikata na watan Agusta harda na wadanda ke kananan hukumomi.

Mista Abubakar Shekara, darakta janar na harkokin labarai a jihar, ya bayyana hakan a wata sanarwa ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a sokoto a ranar Talata.

Shekara ya bayyana cewa anyi wannan umurni ne domin ma’aikata suyi hidimar babban Sallah cikin kwanciyar hankali.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel