Matasan Arewa su marawa Saraki baya sun gargadi Oshiomole akan maganganun da yake furtawa
Kungiyar matasan arew akan zaman lafiya da tsaro mai suna, Arewa Youths for Peace and Security (AYPS), sun kaddamar da goyon bayansu ga shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki da sauran shugabannin majalisar dattawa.
Da yake jawabi ga manema labarai a ranar Laraba a Kano, shugaban kungiyar na kasa Alhaji Salisu, Magaji ya bayyana cewa daga dukkanin rahoto da ke a bayyane, majalisar dattawa ta yanzu ta gabatar da hakokin da suka rataya a wuyarta don haka kamata yayi a yaba mata ba wai a tozarta ta ba.
Ya soki mamayar da jami’an yan sandan farin kaya suka kai majalisar a makon da ya gabata cewa karara hakan ya sabama damokradiyya wanda bai kamata ace hakan ya faru ba.
Magaji ya ja hankalin sanatocin arewa akan nisanta kansu daga duk makircin da ake kullawa domin a tsige Saraki daga shugabantar majalisar dattawa.
Ya shawarce su da su sasanta matsala a tsakaninsu ba kamar yadda shugaban jamiyyar APC na kasa, Adams Oshiomholeke ingiza lamarin ba.
Sun kuma gargadi Oshiomole akan maganganun da yake furtawa
A baya Legit.ng ta hoto cewa Shugaban jam’iyyar All Progressives Congress (APC), Adams Oshiomhole yace ko kotu ba zata iya ceto shugaban majalisar dattawa Bukola Saraki ba.
KU KARANTA KUMA: Halin ba sani ba sabo: Ministoci sun cika da tsoron Osinbajo
Oshiomhole ya bayyana hakan a jiya, Talata, 14 ga watan Agusta a Abuja lokacin da kwamitin jam’iyyar ta gana da masu ruwa da tsaki a majalisar dokoki kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng