Alhamdulillah: Farashin kayan abinci ya yi rugu rugu a wata jihar Arewacin Najeriya

Alhamdulillah: Farashin kayan abinci ya yi rugu rugu a wata jihar Arewacin Najeriya

Kamfanin dillancin labarum Najeriya, NAN, ta ruwaito farashin kayan abinci da na masarufi sun fara karyewa a jihar Nassarawa sakamakon manoma sun fara fitar da abincin da suka noma zuwa kasuwanni.

Wani bincike da majiyar Legit.ng tayi a ranar Laraba, 15 ga watan Agusta a kasuwannin karamar hukumar Keffi ya bayyana mata cewa farashin shinkafar Hausa da masara sun sauko, yayin da farashin shinkafar gida ke cigaba da tsayawa a matsayinta.

KU KARANTA: Zuba hannun jari: Yan kasuwar Turkiyya zasu kafa matatar man fetir a Najeriya

Rahoton ya nuna farashin Masara ya dawo N13,000 zuwa N12,000 akan kowanni buhu, ba kamar kwanakin baya ba da ake sayar da shi akan kudi N15,000, inda a yanzu ake sayar da mudu akan N120, alhali a watanni uku da suka gabata N150 yake.

Mudun shinkafa kuwa da ake sayar da shi akan kudi N400 ya sauko zuwa N400 har ma N350. Wani mazaunin garin Keffi Abubakar Adamu ya bayyana farin cikinsa da yadda aka samu noma mai albarka, wanda hakan ne ke karya farashin abincin.

“Karyewar farashin abincin zai rage wahalhalun da mutane ke ciki a jihar Nassarawa da ma kasa gaba daya, a baya jama’a sun sha wahala a lokacin da farashin abin yayi sama, har ta kai ga wasu ma basa iya ciyar da iyalansu.” Inji shi.

Ita kuwa wata mata mai suna Cecelia Joseph cewa ta yi “Mun yi farin ciki da saukowar farashin abinci, amma har yanzu shinkafar kasar waje bata sauko ba, mun rasa dalili?”

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel