Yi wa SARS garambawul da wasu abubuwa da Osinbajo yayi bayan ya zama Mukaddashin Shugaban kasa
Yanzu haka dai Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbajo ne rike da Najeriya bayan Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tafi hutun sa na shekara a Birnin Landan, Mun kawo maku jerin asu manyan ayyuka da Osinbajo yayi a ofis.
1. Ba da umarnin yi wa SARS garambawul
Mukaddashin Shugaban kasa Yemi Osinbajo ya nemi Shugaban ‘Yan Sandan Najeriya Ibrahim K. Idris ya sakewa Jami’an tsaro na SARS zama. Osinbajo ya bada wannan umarni ne saboda cin zarafin jama’a da SARS ke yi a kasar.
KU KARANTA: Buhari ya doke tarihin da 'Yaradua ya bari a ofis
2. Bada kwangilar wani babban titi a Arewa
A taron FEC ta Majalisar zartarwa da Farfesa Yemi Osinbajo ya jagoranta a makon can, an bada aikin titin Akwanga-Jos-Bauchi-Gombe. Wannan babban aiki da Gwamnatin Tarayya za tayi zai ci kudi har kusan Naira Biliyan 350.
3. Tsige Lawal Daura daga Shugaban DSS
Wani babban mataki da shi ne sallamar Lawal Daura daga matsayin Shugaban Jami’an tsaro na DSS masu fararen kaya. A Ranar Talatar da ta wuce ne aka ji kwatsam Mukaddashin Shugaban kasar ya kori Daura bayan DSS sun zagaye Majalisa.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng