Bahallatsar matar da ta kashe Mijinta: Maryam Sanda ta rada ma jaririnta suna Bilyaminu
Karshe tika tika tik, daga karshe Maryam Sanda, matar nan da ake zargi da kashe Mijinta, ta rada ma jaririn da ta haifa sunan mamacin, wato Bilyaminu, kamar yadda jaridar Daily Nigerian ta ruwaito.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito a ranar Talatar da gabata ne Maryam ta haifi Da namiji, wanda wasu danginta suka tabbatar da cewa Maryam ta rada ma yaron suna Bilyaminu.
KU KARANTA: Babban sufetan Yansanda ya kaddamar da garambawul ga rundunar SARS bisa umarnin Osibanjo
Ita dai Maryam ana zarginta da kashe Mijinta Bilyaminu Muhammad ne ta hanyar caka masa a mazakutarsa da kirjinsa sakamakon wani sabani da suka samu a tsakaninsu a ranar 19 ga watan Nwaumbar 2017.
Sai dai wata babbar kotun tarayya dake Abuja, dake karkashin ikon mai shari’a Halilu Yusuf ta bada belin Maryam a ranar 7 ga watan Maris bisa dalilan tana dauke da ciki.
A tare da Maryam, akwai mahaifyarta, Maimuna Aliyu, kaninta, Aliyu da Sadiya Aminu, yar aikinta, wanda dukkaninsu ake tuhumarsu da hannu cikin kisan mamacin.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng