"Kasashen duniya ba su son Shugaba Buhari ya zarce a 2019"
Da safiyar yau ne dai aka tashi da wani labari a wata jarida dake a Najeriya da ke cewa kasashen duniya da dama ciki kuwa hadda Amurka, Saudiyya da ma tarayyar kasashen turai suna cigaba da matsin lamba ga Shugaba Buhari kada ya nemi takarar tazarce a 2019.
To sai dai tuni fadar shugaban kasar ta fito ta karyata batun ta bakin mai taimakawa shugaban kasar ta hanyar sadarwa, Malam Garba Shehu wanda yace labarin kazon kurege ne kawai.
KU KARANTA: Malaman Arewa sun shirya yadda za su murkushe shi'a
Legit.ng ta samu cewa a watannin baya ne dai shugaba Muhammadu Buhari ya sanarwa da jiga-jigan jam'iyyar sa ta APC aniyar sa ta sake tsayawa takara a zaben 2019.
A wani labarin kuma, Wata tsohuwa mai suna Grace Osagie kamar yadda muka samu daga majiyoyin mu ance wai ta fadi a some a filin jirgin kasa da kasa na jihar Benin inda taje domin tarbar tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar.
Kamar dai yadda wani ganau ya shaidawa majiyar mu, yace ana kyautata zaton tsabar zafin rana ne ya sa matar suma biyo bayan cincirindon magoya bayan fitaccen dan siyasar da suka je tarbar sa.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng