Gwarama: Wani mutum ya maka surikinsa a kotu

Gwarama: Wani mutum ya maka surikinsa a kotu

- Dalilin dauke masa mata ya kai karar mahaifin matarsa kara kotu

- Sai dai surikin nasa ya bayyana dalilin da yasa ya dauke 'yar tasa

- Kotu kuma ta bayar da umarnin kai matar asibiti don fadada bincike

Wani magidanci mai suna Haruna Ali mai shekaru 35 ya kai karar mahaifin matar sa Adamu Mai-Takaima kotun shari’ar Musulunci dake Magajin Gari a garin Kaduna kan zargin sace masa mata.

Gwarama: Wani mutum ya maka sirikinsa a kotu
Gwarama: Wani mutum ya maka sirikinsa a kotu

Haruna ya bayyanawa kotun cewa yau matar sa Hadiza Haruna ta yi watanni 11 a gidan mahaifinta da sunan rashin lafiya sannan ta bar gidansa ba tare da izininsa ba.

” Ni dai ina rokon kotu da ta dawo mini da matata. Zan kula da lafiyar ta da kaina idan bata da lafiya ne" In Ji Haruna.

KU KARANTA: Kalli hotuna da bidiyon yadda ruwa ya tafka gyara a Legas

A nasa bangaren mahaifin Hadiza, Mai-Takaima, ya ce tabas Hadiza bata da lafiya kuma tayi tsawon watanin 11 a gidan sa tana jinyar barin cikin da ta yi sau biyu.

Mai-Takaima ya kara da cewa a duk lokacin da Hadiza za ta baro gidan mijin ta Haruna zuwa gidansa sai ta nemi izinin mijinta.

Bayan ya kammala duba sakamakon gwajin cutar da Hadiza take dauke da shi, Alkalin kotun Musa Sa’ad ya yanke hukuncin canza wa Hadiza asibiti domin a duba cutar yoyon fitsari da take fama dashi don tabbatar da samun lafiyarta. Sannan shi kuma Haruna zai biya duk kudaden asibitin da ya kamata a biya.

Dagan an ne mai shari’ar ya dage sauraron shari’ar zuwa ranar 11 ga watan Satumba.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng