Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un: Hajiya Mahadiyya Baba-Ahmad ta cika

Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un: Hajiya Mahadiyya Baba-Ahmad ta cika

Labari ya kai gare mu cewa Mutanen Garin Zariya sun yi wani babban rashin da ba ya kirguwa a yau dinnan. Hajiya Mahadiyya Baba Ahmad da aka sani da aikin Allah ce Ubangiji yayi wa rasuwa dazu.

Innalillahi wa'inna Ilaihi Raji'un: Hajiya Mahadiyya Baba-Ahmad ta cika
Mahadiyya Baba-Ahmed mai shekaru 68 ta bar Duniya

Hajiya Mahadiyya Baba Ahmad wanda aka sani a Zaria da yi wa addini hidima ta bar Duniya da safiyar Talatar nan. Kawo yanzu dai ba mu da labarin cewa Marigayayiyar tayi fama da wata jinya ko kuma larurar rashin lafiya.

Wannan Baiwar Allah Hajiya Mahadiyya Baba-Ahmad da ta riga mu gidan gaskiya, ita ce babbar ‘Diyar Marigayi Shehin Malamin nan da aka yi a kasar Zaria watau Babba-Ahmed. Asalin su dai Mutanen Kasar Mauritaniya ne.

KU KARANTA: Abin da aka samu a akawun din Janar Murtala bayan an kashe sa a 1976

Kwanakin baya ne Mahmoon Baba-Ahmed wanda shi ne babba a gidan Marigayi Baba-Ahmed ya rasu. Allah yayi yanzu ‘yar uwar sa Mahadiyya ta bi shi zuwa gidan da kowa zai je bayan tayi sallama da Duniya a yau dinnan.

Wannan Dattijuwa Mahadiyya Baba-Ahmed mai shekaru kusan 70 ta yi karatun Arabi da Addini da Boko. Tayi karatun Boko ne a Babban Dodo har ta samu shiga Jami’ar Ahmadu Bello ta Zaria ta karanci harkar shari’ar Musulunci.

KU KARANTA: Labarin 'Yan gidan Baba Ahmad na cikin Garin Zariya

Baba-Ahmed ta dukufa wajen yi wa addini kokari da taimakon marayu da marasa karfi. A shekarar nan Mahadiyya Baba-Ahmed tayi hira da 'Yan jarida inda ta bayyana cewa su 33 aka haifa a gidan su. Yanzu dai su 21 rak ne su ka rage.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng