Siyasar kudi: An zargi Gwamnonin APC da kashe Naira Biliyan 2 domin lashe zabe

Siyasar kudi: An zargi Gwamnonin APC da kashe Naira Biliyan 2 domin lashe zabe

Mun samu labari cewa wani Jam’iyyar adawa ta GPN a Jihar Bauchi ya zargi Jam’iyyar APC mai mulki da kashe makudan kudi domin sayen kuri’un Talakawa a zaben Sanatan da aka yi kwanan nan.

Siyasar kudi: An zargi Gwamnonin APC da kashe Naira Biliyan 2 domin lashe zabe
Sani Malami yace APC ta saye kuri'ar Talakawa a zaben Bauchi

Farfesa Sani Malami wanda yake neman Gwamnan Jihar Bauchi a karkashin Jam’iyyar adawa ta GPN yayi magana game da zaben Majalisar Dattawa na Yankin Kudancin Bauchi da aka yi a karshen makon nan wanda Jam’iyyar APC tayi nasara.

Sani Malami a shafin sa na Facebook yace sun sha kashi ne a dalilin kudin da Gwamnonin jam’iyyar APC mai mulki su ka kashe wajen zaben. Farfesa Malami yace Gwamnonin APC 5 sun kashe fiye da Biliyan 2 wajen sayen kuri’un Bayin Allah.

Malami wanda yake tare da tsohon Gwamnan Jihar ta Bauchi Malam Isa Yuguda ya bayyana cewa Jam’iyyar su ba ta sha kasa wai don Shugaba Buhari ya taka har Bauchi yayi wa ‘Dan takarar APC Lawal Gumau kamfe ba sai dai don kudin da aka kashe.

KU KARANTA: Sanatocin APC na neman karawa Bukola Saraki ciwon kai a Majalisa

Siyasar kudi: An zargi Gwamnonin APC da kashe Naira Biliyan 2 domin lashe zabe
Farfesa Malami yace an yi amfani da kudi wajen murde zaben Bauchi

Honarabul Lawal Yahaya Gumau wanda yanzu ya ke wakiltar Yankin Toro a Majalisar Wakilai ta Tarayya ne ya lashe zaben da aka yi da kuri’u sama da 110, 000. Malami wanda yake Jam’iyyar GPN yace APC ta kashe makudan kudi ne wajen sayen kuri’u.

Tsohon Kwamishinan lafiya na Jihar wanda yanzu ya koma Jam’iyyar GPN watau Farfesa Sani Malami yace APC ta kashe Biliyoyi ne wajen sayen kuri’u saboda halin da Gwamnatin nan ta jefa mutane ciki na yunwa da wahala. Malami yace ba su karaya ba.

A Jihar Katsina inda APC ma ta lashe zaben kujerar Sanatan Arewacin Jihar, Jam’iyyar PDP tace an yi amfani da Jami’an Gwamnati da kuma Sarakunan gargajiya wajen murde zaben Majalisar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng