Najeriya na smaun adadin haihuwar yara miliyan 7 kowace shekara- UNICEF
Asusun Tallafawa Kananan Yara na Majalisar Dinkin Duniya (UNICEF) ya tattara bayanan adadin haihuwar shekara shekara a Nigeria zuwa Miliyan 7 a wannan shekarar.
Hakan na zuwa ne a wani taro na ranar kungiyar “Africa Civil Registration and Vital Statistics (CRVS) da ya gudana a Abuja.
Adadin haihuwa a Nigeria ya kai adadin yawan Al’umar kasar Rwanda, wanda hakan ke nuni da cewa yaran da ake Haifa a Nigeria a kowace shekara zasu iya hada kasa guda daya.
Da yake jawabin a wajen taron, wakilin UNICEF a Nigeria, Mohammed Fall, yace ya kamata Nigeria ta inganta fannin rejistar mutane da kuma muhimman bayanansu tun a lokacin haihuwa da kuma lokacin mutuwarsu don magance matsalolin yawan jama’ar dake cikin kasar.
KU KARANTA: Dalilin da yasa na ziyarci Obasanjo – Bukola Saraki
Shugaban Hukumar Kidaya ta kasa NPC, Mr. Eze Druiheoma, yace Nigeria zata fara yin cikakkiyar rejistar Haihuwa da Mutuwa a cibiyoyin hukumar 3,600 dake fadin kasar.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng