Lamari yayi tsamari yayin zanga-zangar kasuwar 'yan waya ta Kano (Hotuna)
- A wani yanayi mai cike da sarkakiya, wani mutum ya bayyana da izinin kotu dake nuna hamshakiyar kasuwar waya ta Farm Center ta zama mallakarsa
- Sai dai 'yan kasuwar sunyi tir da kuma fatali da wannan ikirari nasa
- Kana su kayi kira ga mahukunta da su shigo cikin maganar domin nemowa maganar mafita
A safiyar yau ne ‘yan kasuwar waya ta Farm Center dake Kano suka gudanar da zanga-zangar kin amincewa da ikirarin tashinsu da wani attajiri mai suna Alhaji Muntari yayi daga kasuwar baki daya.
‘Yan kasuwar sun yi bore gami da tabbatar da cigaba da kasuwancinsu na neman halak a kasuwar, duk da takardar izinin mallaka da Alhaji Muntarin ya zo da ita daga kotun da mai shari’a Khadija Aboki ke jagoranta.
Babbar kasuwar da yanzu haka babu kamar ta a duk fadin yankin Arewacin Najeriya, an gina ta ne lokacin mulkin tsohon gwamnan Kano Malam Ibrahim Shekarau.
Gwamnan na Kano a wancan lokaci ya kafa kwamitin da zai gano hanyar da za’a magance cunkoson ababen hawa da kasuwar take haifarwa tare da kuma fadada ta don samawa matasan jihar aikin yi.
Ana shi jawabin Sakataren kasuwar ta Farm Center Yusuf Sulaiman (Anderson) ya bayyana matakin da suke shirin dauka domin ganin dumbun matasan dake sana’a a kasuwar sun cigaba ba tare da tsaiko ba.
“Ko dai gwamnati ta biya Alhaji Muntari, mu kuma muna biyanta haya; ko kuma a kira banki ya sayi kasuwar mu kuma muna biya a hankali ko kuma asan yadda za’ai da mu amma babu maganar tashi”.
Wani matashin dan kasuwa Sunusi Yusuf da wakilinmu ya zanta da shi kan yadda yake kallon matakin da ake shirin dauka na kwace kasuwar daga gare su, ya tabbatar da cewa, “Ko kusa bamu laminta da wannan hukuncin ba, kasancewar bamu da labarin lokacin da aka je kotun da ta yanke hukuncin balle a gayyace ‘yan kasuwa ko lauyoyinmu don jin ba’asimu.
Yanzu haka dai kasuwar ta Farm Center na kunsar sama da mutane 10,000 a kullum da suke gudanar da sana’oi daban-daban kama daga kan siyarwa da gyaran wayar salula, Kwamfuta da kayan sawa da Takalma da layuka da katin waya da sauransu.
Rahotanni sun tabbatar da cewa an cimma yarjejeniyar tarewa a kasuwar ne a wani yanayi mai cike da sarkakiya a shekarar 2008 tsakanin Alhaji muntarin da gwamnatin wancan lokacin da kuma ‘yan kasuwar.
Yanzu haka dai ‘yan kasuwar sun shafe shekaru hudu suna rikici mallakar, kafin zuwa da dokar kotu na lallai su tashi daga kasuwar, ta zama ta Alhaji Muntari kuma yana da ikon sauya mata fasali yadda yake so.
Haka zalika gwamnatin Kano ta hannun hukumar KNUPDA za su biya tarar Naira Miliyan N1m saboda kin tashi bayan yarjejeniyar zaman 'yan kasuwar ta kare kamar yadda aka tsara tun farko.
Wakilinmu yayi kokarin jin ta bakin Alhaji Muntari don yayi karin haske kan lamari, amma yaki amsa wayar sa.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng