Labari mai dadi yayinda NEMA ta bayar da tallafin motoci 8 na kayan agaji ga mutane 29,000 a Zamfara

Labari mai dadi yayinda NEMA ta bayar da tallafin motoci 8 na kayan agaji ga mutane 29,000 a Zamfara

Hukumar bayar da agajin gaggawa (NEMA) ta bayar da tallafi na motoci takwas cike da kayan agaji ga kimanin mutane 29,000 ga mutanen da harin yan fashi ya shafa a kauyuka bakwai da garuruwa a masarautar Anka, Zamfara.

Shugaban NEMA, sashin Sokoto, Mallam Sulaiman Muhammad ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labaran Najeriya a Gusau a ranar Litinin, 13 ga watan Agusta.

Labari mai dadi yayinda NEMA ta bayar da tallafin motoci 8 na kayan agaji ga mutane 29,000 a Zamfara

Labari mai dadi yayinda NEMA ta bayar da tallafin motoci 8 na kayan agaji ga mutane 29,000 a Zamfara
Source: Depositphotos

Sulaiman yace kayayyakin sun hada da hatsi, kayayyakin sawa, kayan kwaliyya da kayan bandaki da sauransu.

KU KARANTA KUMA: Kuma dai, masu zanga-zanga sun kunyata Kwankwaso sunyi masa ihun ‘Sai Buhari’ a filin jirgi (bidiyo)

A cewarsa, mukaddashin shugaban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo da darakta-janar na hukumar NEMA ne zasu jagoranci rabon kayayyakin gay an gudun hijiraa a karamar hukumar Talata-Mafara dake jihar a ranar Talata, 14 ga watan Agusta.

Yace hakan taimako ne domin sanya walwala a fuskokin wadanda abun ya cika dasu.

Sulaiman ya kuma yi godiya ga gwamnati da sarakunan yankin bisa irin gudunmawa da suke ba yan gudun hijira.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel