Sarkin Kano yayi lugude kan ‘yan siyasa masu ci-da-addini

Sarkin Kano yayi lugude kan ‘yan siyasa masu ci-da-addini

- An budewa 'yan siyasar Arewacin Najeria aiki

- Mai martaba Sarkin Kano Malam Muhammadu Sunusi II ya bayyana alakar rashin cigaba da siyasar ci-da-addini ko al'ada

- Sarkin ya furta zancen ne a yayin wani taro a jihar Katsina

Mai martaba Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II, yayi kira ga 'yan siyasa da su daina fakewa da addini wajen musgunawa al'ummar Najeriya.

Sarkin Kano yayi lugude kan ‘yan siyasa masu ci-da-addini
Sarkin Kano yayi lugude kan ‘yan siyasa masu ci-da-addini

Sarkin ya nuna damuwarsa musamman ga yankin arewacin kasar nan, ganin yadda wasu ke amfani da addini da al'ada domin cimma burin kansu.

Ya kara da cewa ‘yan siyasar yanzu sun maida hankalinsu wajen amfani da addini, inda har su kanyi alkawari daban-daban na za su kawo cigaba da sunan addini, maimakon maida hankali akan abinda ya shafi ilimi da harkar lafiya, wanda hakan ke haifar da nakasu tare da koma baya ga jihohi da dama a yankin.

KU KARANTA: Kwastam tayi babbar nasarar damke maganin Kodin, tsala-tsalan motoci da wasu mutane 8

Sunusi Lamido ya kara da cewa ba abin mamaki bane ganin duk jahohin da ake amfani da su wajen ci-da-addini su ne kan gaba wajen koma baya ta fuskar abinda ya shafi tattalin arziki, don haka dole tunanin mutane ya sauya.

Mai martabar yayi wannan kira ne a yayin da yake jawabi a taron matasa na duniya wanda aka gudanar a jihar Katsina a cibiyar koyar da sana'o'in dogaro da kai da marigayi tsohon shugaban hukumar ‘yan sanda ta kasa M. D Yusif ya kafa don tallafawa nakasassu.

Dagan an ne Sarkin Kanon yayi kira ga gwamnati wajen ganin ta jawo matasa cikin harkokin da suka shafi harkar Noma don tabbatar da cigabamai dorewa.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng