Zaben Daura: Ba za mu amince da sakamakon INEC ba – Inji PDP

Zaben Daura: Ba za mu amince da sakamakon INEC ba – Inji PDP

Mun samu labari daga Jaridar Punch cewa Jam’iyyar adawa ta PDP ta huro wuta bayan Hukumar INEC ta sanar da sakamakon zabukan Majalisa da aka yi. PDP tace a-ta-fau ba ta yarda da zabukan da aka yi ba.

Zaben Daura: Ba za mu amince da sakamakon INEC ba – Inji PDP

APC tayi amfani da karfin mulki da iko a zaben Katsina Inji PDP

Shugaban Jam’iyyar PDP na Jihar Katsina Salisu Yusuf Majigiri ya bayyana cewa ba ayi gaskiya a zaben Sanatan Yankin Daura da aka gudabar a karshen makon jiya ba. Honarabul Ahmad Babba-Kaita ya lashe zaben ‘Dan Majalisar Yankin.

PDP tace za ta garzaya Kotu saboda zaben bai da inganci a dalilin saida kuri’u da aka ika yi domin Jam’iyyar APC mai mulki tayi nasara. PDP tace an yi irin abin da aka yi a Jihar Ekiti ne a wajen zaben na Sanatan Arewacin Jihar Katsina.

KU KARANTA: Ana neman kama Shugaban Hukumar zabe na kasa

Jam’iyyar PDP za ta shigar da kara a Kotu ne a fito mata da hakkin ta. PDP tace an yi amfani da Jami’an Gwamnati da kuma Sarakunan gargajiya wajen murde zaben Majalisar. PDP tace ba za ta bari irin haka ya cigaba da faruwa a 2019 ba.

Jam’iyyar APC ce ta lashe zabukan Majalisa da aka yi a Katsina, Bauchi da Kogi. PDP ma a Jihar Kogi tace za ta shigar da kara bayan Haruna Isa na APC ya lashe zaben. A Bauchi ma Honarabul Lawal Yahaya Gumau na APC ne yayi nasara.

Jam’in INEC Hudu Ayuba-Abdullahi ya tabbatar da cewa APC tayi nasara da kuir’a 224,607. Alhaji Kabir Babba Kaita mai kuri’u 59,724 ya sha kasa hannun kanin sa Ahmad babba Kaita.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Legit

Tags:
Mailfire view pixel