Kalli fuskokin gwarazan Yansanda 4 da masu garkuwa da mutane suka kashesu a Kaduna

Kalli fuskokin gwarazan Yansanda 4 da masu garkuwa da mutane suka kashesu a Kaduna

A jiya, Lahadi, 12 ga watan Agusta ne wasu gungun yan bindiga masu garkuwa da mutane suka yi ma wasu Yansanda kwantan bauna a wani daji dake garin Rigasa na jihar Kaduna, suka kashe gwarazan Yansanda har guda hudu.

Legit.ng ta ruwaito kwamandan tawagar Yansandan, mataimakin kwamishina Abba Kyari ya tabbatar da kisan Yaran nasa guda hudu a shafinsa na Facebook, inda yace lamarin ya faru ne da sanyin safiyar Lahadi, bayan sun kamo wasu barayin mutane da suka yi garkuwa da Sheikh Ahmad Al-Garkawy.

KU KARANTA: Mayakan rundunar Sojan kasa sun yi bore, sun kulle filin sauka da tashin jirage na Maiduguri

Kalli fuskokin gwarazan Yansanda 4 da masu garkuwa da mutane suka kashesu a Kaduna

Yansandan

Kyari ya bayyana sunayen mamatan kamar haka:

AP/No. 148333 Inspekta Benard Odibo

AP/No. 181539 Inspekta Mamman Abubakar

AP/No. 192938 Inspekta Haruna Ibrahim

F/No. 267815 Sajan Emmanuel Istifanus

Kalli fuskokin gwarazan Yansanda 4 da masu garkuwa da mutane suka kashesu a Kaduna

Yansandan

Sai dai Kyari ya kara da cewa a yayin musayar da wutar da aka kashe Yansandan hudu, suma sun yi nasarar bindige yan bindiga guda shidda, yayin da Dansanda daya da ya samu rauni ya samu kulawa a Asibiti kuma an sako shi.

Daga karshe Kyari ya kara da cewa rundunar Yansanda na bin sawun yan bindigan don tabbatar da ta kama su, tare da hukuntasu yadda ya kamata.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel