Ikon Allah: Yaro dan baiwa da ya rayu shi kadai a wani hadarin Jirgin sama

Ikon Allah: Yaro dan baiwa da ya rayu shi kadai a wani hadarin Jirgin sama

- Zakaran da Allah ya nufa da cara ko ana Muzuru ana Shaho sai yayi

- Da kwanan wani yaro karami a Duniya, bayan hadarin Jirgin sama ya rutsa da shi

A safiyar jiya Lahadi ne jami'an ceto suka gano wani yaro dan kimanin shekaru 12 a duniya kwance a gurin da aka yi wani hatsarin Jirgin sama a kasar Indonesia.

Ikon Allah: Yaro dan baiwa da ya rayu shi kadai a wani hadarin Jirgin saman
Ikon Allah: Yaro dan baiwa da ya rayu shi kadai a wani hadarin Jirgin saman

Na'urar kyamarar hoto ta nuno yaron cikin rai kwakwai-mutu-kwakwai.

Tun da farko dai masu ceton sun same shi a cikin bangorin Jirgin saman ne da ya fado kasa akan iyakar kasar Papua Guinea.

KU KARANTA: Mummunar musayar wuta da ‘yan bindiga, ‘yan sanda 4 sun rasu a Kaduna

Bugu da kari an bayyana cewa matukin jirgin ya samu tangardar na'ura ne daga filin jirgin sama na Oksibil, inda yake samun umarnin tuki.

Dama akwai tarihin hatsarin Jirgin sama da ya faru a dai-dai iyakar kasar ta Guinea da kuma Indonesia, wanda hakan yana faruwa ne a dalilin rashin kyawun yanayi. Domin ko a shekarar 2015 sai da aka samu hatsarin jirgin sama wanda ya lashe rayukan mutane 54.

Kawo yanzu dai babu wasu rahotanni ko binciken da ya tabbatar da musababin faduwar jirgin.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng