Masu sana’ar kifi na gamuwa da kalubale ta ko ina a Yankin Borno

Masu sana’ar kifi na gamuwa da kalubale ta ko ina a Yankin Borno

Har yanzu ana fama da ‘Yan ta’addan Boko Haram a Yankin Arewa maso Gabashin Najeriya musamman wajen harkar su. ‘Yan ta’addan na sa wa Masunta takunkumi kafin su iya shiga ruwa wanda hakan ya jawo kayan abincin su ka yi tsada.

Masu sana’ar kifi na gamuwa da kalubale ta ko ina a Yankin Borno
Masunta a tafkin Chadi su na gamuwa da cikas na sha'anin tsaro

Jama’a da dama na amfani da tafkin Chadi wajen farautar dabbobin ruwa a baya, sai dai ‘Yan ta’addan Boko Haram na tare hanyoyin Yankin su na tatsar jama’a babu gaira babu dalili wanda hakan ya jawo raguwar masu sana’ar su a Yankin kasar.

‘Yan Jaridar kasar waje sun rahoto cewa Masunta kan shiga ruwan Chadi ne a boye domin gudun kar su fada hannun ‘Yan ta’addan Boko Haram duk da kokarin da Sojojin Najeriya su kayi na inganta harkar tsaro a Yankin na Arewa maso Gabas.

KU KARANTA: Wani tsohon Gwamna ya fice daga Jam'iyyar APC

Wani Bawan Allah mai suna Aminu Mohammed ya fadawa gidan yada labarai na AFP cewa su na fuskantar barazana a sana’ar su musamman a halin yanzu zuwa lokacin da ake sa ran Sojojin Najeriya za su gama fatattakar ‘Yan Boko Haram.

Wani Masunci a Yankin Baga ya bayyanawa ‘Yan jarida cewa Sojoji sun tare motocin da ke dauke da kifin sa na sama da Naira Miliyan 2. Bayan wahalar farautar da ake sha, Jami’an tsaro kan karbe kifi da karfin tsiya daga hannun ‘Yan kasuwa a Yankin.

‘Yan Boko Haram kuma kan hana jama’a shiga ruwa domin su har sai sun biya kudi N10,000. Wani wanda sana’ar sa kenan ya bayyawa ‘Yan Jarida wannan. Hakan ya sa Sojoji ke tsare wasu ‘Yan kasuwa da sunan su na agazawa ‘Yan ta’adda da kudi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng