Jam’iyyar APC za ta lashe kujerar Sanatan Yankin Daura Mahaifar Shugaba Buhari

Jam’iyyar APC za ta lashe kujerar Sanatan Yankin Daura Mahaifar Shugaba Buhari

Dazu kun ji labari cewa Jam’iyyar APC mai mulki ta kama hanyar lashe zaben wasu ‘Yan Majalisu da aka yi a Arewa Jihohin Bauchi da kuma Katsina da ma Jihar Kogi a karshen wannan mako.

Jam’iyyar APC za ta lashe kujerar Sanatan Yankin Daura Mahaifar Shugaba Buhari

Ahmad Babba Kaita zai doke ‘Dan uwan sa a zaben Daura. Hoto daga: Bashir Ahmaad

Hukumar INEC ta gudanar da zaben Sanatocin da za su wakilci Kudancin Jihar Bauchi da kuma Arewacin Jihar Katsina Yankin Buhari. Hakan na zuwa ne bayan ‘Yan Majalisun da ke wakiltar Yankin sun rasu kwanakin baya.

A Jihar Katsina inda aka yi zaben kujerar Sanatan Yankin Daura da kewaye, Honarabul Ahmad Babba Kaita ne yake kan hanyar zama Sanata. ‘Dan takarar na APC ya samu kuri’un da su ka zarce na Abokin takarar sa da ke Jam'iyyar PDP.

INEC ta fitar da sakamakon zaben akwatin Unguwar Sarkin Yara ‘A’ wanda nan ne inda Shugaban kasa Buhari yake zabe. Jam’iyyar APC ta samu kuri’a 1984 yayin da PDP kuma ta tashi da kuri’u 255, Jam’iyyar GPN tana da kuri’a 182.

KU KARANTA: 'Yan gida guda za su gwabza takara a Jihar Katsina

A wasu akwatunan ma kamar yadda mu ka samu labari, Jam’iyyar PDP mai adawa ta samu kuri’a 1 ne kacal inda APC mai mulki ta lashe kuri’u sama da 200. Jam’iyyar GPN ta taka rawar gani a zaben da aka yi inda ta rika kalo kuri’u.

Honarabul Ahmad Babba Kaita shi ne ‘Dan Majalisar Wakilan Tarayya na Yankin Kankiya/Ingawa/Kusada. Ahmad yayi takara ne da ‘Dan uwan sa Kabir Babba Kaita. Idan APC ta samu nasara za ta kara yawa a Majalisar Dattawa.

Dama can kun ji cewa Tsohon Gwamnan Bauchi Isa Yuguda zai sha kasa a hannun ‘Dan takarar APC Lawal Yahaya Gumau a zaben Sanatan Bauchi ta Kudu. Yanzu haka dai Shugaba Buhari bai yi wannan zabe ba domin ba ya kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel