Jam’iyyar APC na daf da lashe zaben Sanatan Bauchi ta Kudu
A halin yanzu dai labarin da mu ke ji shi ne Jam’iyyar APC mai mulki ta kama hanyar lashe zaben wasu ‘Yan Majalisu da aka yi a Jihohin Bauchi da kuma Katsina a karshen makon nan.
Ko da dai ba a sanar da sakamakon zaben ba kawo yanzu, Sakataren yada labarai na Jam’iyyar APC Yekini Nabena ya bayyana godiyar sa ga mutanen wadannan Yankin inda yake nuna cewa APC ce ta lashe zabukan da aka yi jiya Asabar.
Ana tunani ‘Dan takarar APC na zaben Sanatan Bauchi ta Kudu watau Lawal Yahaya Gumau ya sha gaban ‘Dan takarar da ke neman Sanatan a kujerar GNP watau Isa Yuguda. Sauran ‘Yan takarar sun hada da Haruna Ayuba da Aminu Tukur.
KU KARANTA: Babu wanda ya isa ya tsige su Saraki a Majalisa - PDP
‘Da takarar Jam’iyyar APC Honarabul Lawal Yahaya Gumau yace babban aikin da yake so yayi wa mutanen Alkaleri, Bauchi, Toro, Kirfi da kewaye shi ne ya tabbatar cewa an canza tsarin mulki yadda Buhari zai yi mulki na din-din-din.
Lawal Yahaya Gumau tsohon ‘Dan Majalisar dokokin Jihar Bauchi ne. Yanzu haka Honarabul Gumau yana wakiltar Yankin Toro a Majalisar Wakilai ta Tarayya. Za ku tuna cewa Sanatan Yankin watau Ali
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
Ko a http://twitter.com/naijcomhausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Asali: Legit.ng