Borin kunya ke damun Jam’iyyar APC ba wani abu ba – Inji Saraki

Borin kunya ke damun Jam’iyyar APC ba wani abu ba – Inji Saraki

Mun samu labari dazu cewa Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ta bakin wani Hadimin sa yayi kaca-kaca da Jam’iyyar APC mai mulki na sukar shugabancin Majalisar kasar da tayi. Saraki yace ba za a raba masu tunani ba.

Borin kunya ke damun Jam’iyyar APC ba wani abu ba – Inji Saraki

Shugaban Majalisar Dattawa Bukola Saraki ya soki APC

Yusuph Olaniyonu, wanda yake magana da yawun bakin Bukola Saraki ya maidawa APC martamo jiya bayan ta soki Majalisar kasar inda tace abubuwa ba su taba tabarbarewa ba kamar a lokacin da Saraki yake jagoranci a Kasar.

Bukola Saraki yace zargin da Jam’iyyar APC ta ke yi bai da gindin zama sai dai kurum kokarin da ta ke yi na yi wa tsarin Damukaradiyyan kasar hawan kawara. Saraki yace APC tayi kokarin yi wa Majalisa juyin-mulki ne a makon nan.

KU KARANTA: Za mu tsige Bukola Saraki - Shugaban Jam'iyyar APC

A Ranar Talata ne Jami’an DSS su ka zagaye Majalisar Tarayya aka nemi a hana ‘Yan Majalisar Kasar shiga cikin ofisoshin su. Bukola Saraki ya zargi Jam’iyyar APC da kitsa wannan danyan aiki da niyyar canza shugabannin Majalisar.

A jawabin na Yusuph Olaniyonu yace kalaman da Jam’iyyar APC ta yi ta bakin Sakataren yada labaran ta rikon-kwarya Yekini Nabena borin kunya ne bayan yunkurin tsige Bukola Saraki da Mataimakin sa Ike Ekweremadu bai kai ko ina ba.

APC dai ta nemi Saraki ya bar matsayin sa bayan ya sauya sheka ya koma Jam’iyyar PDP wanda ba ta rinjaye a Majalisar Dattawan. Mista Yekini Nabena yace tun farko Bukola Saraki bai cancanta da shugabancin Majalisar kasar nan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel