Duniya mai yayi: An yi ma Kwankwaso ihun ‘Sai Buhari’ a jihar Kaduna (Bidiyo)

Duniya mai yayi: An yi ma Kwankwaso ihun ‘Sai Buhari’ a jihar Kaduna (Bidiyo)

A yau juma’a 10 ga watan Agusta ne tsohon gwamnan jihar Kano, kuma sanatan Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya sha mamaki a jihar Kaduna, inda jama’a suka yi masa ihun sai Baba, Sai Buhari.

Legit.ng ta ruwaito wannan lamari dai ya faru ne a babban Masallacin Juma’a na Salamat, dake kan titin bashama a unguwar Tudun Wada, inda Kwankwaso ya halarci sallar Juma’a.

KU KARANTA: Likafa ta ci gaba: Shugaban majalisar dinkin Duniya ya nada Amaechi babban mukami

Sai dai fitarsa keda wuya daga Masallacin, sai jama’a suka yi masa ihun ‘Sai Baba!’ Sai Buhari!!’, kamar dai yadda ake yi ma shugaban kasa Muhammadu Buhari a duk lokacin da ya shiga cikin jama’a.

Wannan eho da jama’a suka yi ma Kwankwaso ya nuna jam’an basa tare da shi kenan, ma’ana su Buhari ne nasu, shike muradi a siyasance. Wannan ne karo na biyu da aka samu jama’a suna yi ma Kwankwaso wannan ihun tun bayan komawarsa jam’iyyar PDP.

Shi da Kwankwaso ya tare da zama a jihar Kaduna ne tun bayan saukarsa da mukamin gwamnan jihar Kano, sa’annan rikici dake tsakaninsa da gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya hana shi komawa Kanon da zama, don haka zai ya mayar da Kaduna gidansa.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: