Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu satar kudi ta ATM a jihar Kano da Enugu

Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu satar kudi ta ATM a jihar Kano da Enugu

Mun samu rahoton cewa hukumar 'yan sanda ta samun nasarar cafke wasu miyagun mutane da suka shahara da yiwa al'umma satar kudi ta hanyar na'urar da kuma katin nan na ATM cikin birnin Enugu.

Cikin wata sanarwa da kakakin hukumar 'yan sandan jihar ya bayyana, SP Ebere Amaraizu ya bayyana cewa, hukumar ta cafke matasan uku ne da katukan ATM har guda 30 mallakin mutane daban-daban

Kazalika cikin wani rahoto na daban da muka samu ya bayyana cewa, hukumar 'yan sandan jihar Kano ta kuma cafke wasu miyagu masu aikata makamancin wannan mugun hali da suka kware wajen kwashewa mutane kudi yayin da suka je banki domin cirar kudi ta na'urar ATM.

Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu satar kudi ta ATM a jihar Kano da Enugu
Hukumar 'Yan sanda ta cafke masu satar kudi ta ATM a jihar Kano da Enugu

A yayin zayyanawa kakakin hukumar 'yan sandan jihar Kano Magaji Musa Majia hanyoyin su na dabaru da suke bi wajen kwashewa bayin Allah dukiyoyin su sun bayyana cewa, lamari da bai wuci yaudara ba gami da zamba cikin aminci.

A cewar su, "su na zuwa da yawa ne banki yayin da idan mutum yaje cirar kudi kuma suka fahimci sabon shiga ne a harkar latsa nau'rar ta ATM, su kan yaudare sa da basajar taimakon sa da a yayin haka suke sanin lambobin sa na sirri da ya ke amfani da su wajen zarar kudi."

KARANTA KUMA: Dalilin da zai hana Saraki murabus - Bafarawa

"Baya ga haka kuma su kan yi awon gaba da katin mutane bayan sun samu nasarar sanin wannan lambobi na sirri idan su ke ci gaba da bushashar su."

Legit.ng ta fahimci cewa, daya daga cikin masu wannan mugun hali mai sunan Umar Ya'u mai inkiyar ORA, dan gidan wani tsohon ciyaman ne a jihar Jigawa da har ya mallaki mota ta hanyar wannan mummunar sana'a.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng