Wasu ‘Yanuwan juna sun fito takarar Sanatan Katsina a PDP da APC

Wasu ‘Yanuwan juna sun fito takarar Sanatan Katsina a PDP da APC

A karshen makon nan ne Hukumar INEC za ta gudanar da zaben Sanata na Yankin Arewacin Katsina inda za a buga takara tsakanin wasu manyan ‘Yan siyasa da su ka fito daga gida guda a cikin Jihar ta Katsina.

Wasu ‘Yanuwan juna sun fito takarar Sanatan Katsina a PDP da APC

Hon. Ahmad Babba Kaita zai yi takara da 'Dan uwan sa

Ko dai ya ta fadi sha ne ga ‘Yan gidan Babba Kaita a Katsina inda Yaran gidan 2 za su yi takara da juna a zaben Sanatan Yankin Daura a PDP da APC. Honarabul Ahmad Babba Kaita ne zai buga da ‘Dan uwan sa na jini watau Kabir Babba Kaita.

Honarabul Ahmad Babba Kaita tun 2011 yake Majalisa inda yake wakiltar Yankin Kankiya/Ingawa/Kusada. A 2015 ‘Dan uwan sa Kabir Babba yana cikin wadanda su ka yi kokari wajen ganin ya koma kan kujerar sa a karkashin Jam'iyyar APC.

KU KARANTA: Ko kadan ba mu da niyyar tsige Buhari a Majalisa inji Sanatocin PDP

Ahmad Babba Kaita da Kabiru Babba Kaita ‘Yan gida daya ne kuma Mahaifin su daya sai dai banbancin Mahaifiya. Yanzu dai siyasa ta raba kan su inda kowane yake harin kujerar Sanatan Yankin da Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya fito a zaben gobe.

Kamar yadda mu ka samu labari, a 2015 Kabiru Babba ya kashewa ‘Dan uwan sa Miliyoyin kudi wajen ganin ya koma Majalisar Wakilan Tarayya. Yanzu dai kowanen su sai dai ta sa ta fishe sa a wannan zabe da za ayi na Majalisar Dattawan kasar.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel