Har yanzu akwai 'yan mata daga Najeriya da ke maqale a Saudiyya - NAPTIP

Har yanzu akwai 'yan mata daga Najeriya da ke maqale a Saudiyya - NAPTIP

- Gwamnatin tarayya zata dawo da yammata sama da 50 daga Saudi Arabia

- Safarar mutane dai ta zama ruwan dare

- Idan an kaisu kasashen ketaren sukan koma kamar bayi ne

Har yanzu akwai 'yan mata daga Najeriya da ke maqale a Saudiyya - NAPTIP
Har yanzu akwai 'yan mata daga Najeriya da ke maqale a Saudiyya - NAPTIP

Cibiyar yaki da safarar mutane, NAPTIP tace Gwamnatin tarayya zata dawo da sama da yammata 50 da suke a kasar Saudi Arabia.

Darakta Janar na NAPTIP ya fadi haka ne a wata tataunawa da sukayi ranar Alhamis da ministan al'amuran waje, Geoffrey Onyeama, akan sakamakon binciken da akayi akan yammata da akayi safarar su zuwa Saudi Arabia.

Darakta Janar din da ya iso tare da daya daga cikin yammatan da abun ya shafa yace ministan ne ya nada kungiyar bincike bayan korafin da NAPTIP ta kawo mishi akan matasan da aka safarar su zuwa kasar Saudi.

"Munzo maka da koken yanda aka kwashe mana matasa zuwa kasar Saudi Arabia da sunan samun aiki".

"Mun kira wadanda abin ya shafa da suke Saudi, suna cikin mawuyacin hali, sai ka hada kungiyar da ta kunshi jami'an NAPTIP da suka je har Saudi Arabia don bincike.

"Lokacin da kungiyar ta kai kasar, mun samu sama da mata 50 wadanda muka tattauna dasu kuma suka fada mana akwai mata da yawa dake lungunan kasar".

"Daya daga cikin wadanda abin ya shafa ce nan muka taho da ita, zata yi bayani akan abinda suke ciki"

Tace akwai yammatan Najeriya dake can kasar suna aikin bauta a gidajen larabawa.

Kamar yanda tace, da yawan su ana musu fyade, wasu kuma suna aikin awa 18 a cikin awoyi 24 na rana.

DUBA WANNAN: Saudiyya ta kirkiro manhajar tantance wa'azi

Da yawansu suna aikin ma ba'a biyan su kamar yanda yan damfarar da suka kaisu suka fada musu.

Akwai wata babbar hanya da suke samun Visa don yin safarar mutane saboda Idan sahihin kasuwanci ne zai kai mutum, baya samun Visa da sauki.

Ministan ya Kwatanta hakan da abu mafi muni kuma yace Gwamnatin tarayya zata shawo kan matsalar, sannan kuma ta magance ta.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng