Ana wata ga wata: Dino Melaye ya ki bayyana a kotu yau
- Har yanzu tsugunno bai karewa Sanata Dino Melaye ba
- Alkali da lauyoyi sun taru a kotu amma yaki bayyana
- Ana sake sanya wata ranar don cigaba da shari'ar
A karo na biyu dan majalisa mai wakiltar Kogi ta yamma Sanata Dino Melaye ya ki bayyana a yau Laraba gaban kotu domin fuskantar tuhumar da ake masa.
Amma sai dai ragowar mutane biyun da ake tuhumarsu tare Kabir Seidu, wanda aka fi sani aka Osama, da Nuhu Salihu mai inkiya Smally duk sun hallara a kotu.
A zaman kotun da ya gabata alkalin dake sauraren karar Sulyman Abdalah, ya zabi ranar 9 ga watan Agusta domin cigaba da shari’ar bayan da Dino Melayen ya shigar da korafin cewa ak kai masa hari yayinda suke hanyar zuwa Lokoja don amsa gayyatar da jami’an ‘yan sanda suka yi masa.
KU KARANTA: Fitar Saraki, Tambuwal da Ortum ba zai hana Buhari cin zabe ba - APC
A ranar Laraba ne lauyan Melaya Yemi Mohammed ya gabatar da takardar asibiti ga alkalin kotun, amma duk da kin amincewa da lauyan rundunar ‘yan sanda Theophilus Oteme, hakan bai hana mai shari’ar amincewa da daga sauraron karar zuwa yau ba.
Ya zuwa yanzu dai suma ragowar biyun da ake musu shari’a da Dino Melayen sun nemi kotun da ta bayar da su beli kasancewar sun shan azabar laifin da bas u san hawa ba basu san sauka ba.
Daga karshe dai mai shari’a Abdalah ya sake dage shari’ar zuwa 21 ga watan Agustan da muke ciki don duba yiwuwar bayar da belin mutane biyun, sannan kuma ya sanya ranar 20 ga wata don jin da wacce Sanata Dino Melaye zai zo da ita.
Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng