Atiku ne mafi cancanta ya hambarar da Buhari a 2019 - Inji wata kungiyar Yarbawa
Shugaban hadakar kungiyar matasan Yarbawan Najeriya mai suna Cif Jackson Lekan Ojo ya bayyana cewa tsohon mataimakin shugaban kasar Najeriya, Alhaji Atiku Abubakar ya yafi cancanta da ya jagoranci kasar nan ta Najeriya a zabe mai zuwa.
Cif Ojo ya bayyana hakan ne a yayin wata fira da yayi da majiyar mu a garin Abuja inda kuma ya bayyana cewa tuni ya dauki damarar jan ragamar kungiyar ta sa wajen fara yiwa zabin nasa Kamfe da wuri domin samun nasara.
KU KARANTA: Hotunan SHugaba Buhari da Gwamna El-Rufai cikin jirgin kasa
Legit.ng dai ta samu cewa ya kuma kara da cewa kadan daga cikin dalilan sa na fadar haka shine ganin yadda Atiku din ya samarwa da matasa da dama aiyyukan yi a matsayin sa na dan kasuwa sabanin rasa ayyukan yin da shugaba Buhari ya jawowa kasar.
Daga nan ne kuma sai Cif Ojo ya bayyana masu zagin Atiku Abubakar din don ya yanke shawarar barin jam'iyyar ta APC zuwa PDP a matsayin marasa adalci da basu san inda duniya ke tafiya ba.
Idan ka na da wani shawara ko bukatan bamu labari, tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da
Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Sabuwar hanyar karanta labarain Legit.ng HAUSA
Asali: Legit.ng