Shugaban R-APC Buba Galadima ya samu lafiya bayan yayi hadarin mota

Shugaban R-APC Buba Galadima ya samu lafiya bayan yayi hadarin mota

Kwanakin baya idan ba ku manta ba, Injiniya Buba Galadima wanda shi ne Shugaban ‘Yan tawaren Jam’iyyar APC yayi hadarin mota. Yanzu dai mun ji cewa Injiniya Galadima ya fara samun lafiya.

Shugaban R-APC Buba Galadima ya samu lafiya bayan yayi hadarin mota
Buba Galadima tare da Kwankwaso da Bafarawa bayan yayi hadari

Buba Galadima ya samu sauki bayan wani mummunan hadarin mota da yayi a kan hanyar Hadejiya zuwa Kano kusan makonni 2 da su ka wuce. Motar ‘Dan siyasar sai da ta wuntsula sannan ta fado kasa inda aka arce da su zuwa asibiti.

Yanzu Buba Galadima ya fara samun lafiya inda har tsohon Gwamnan Jihar Kano Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kuma Attahiru Dalhatu Bafarawa su ka kai masa ziyara har gidan sa domin su duba sa a cikin farkon wannan makon.

KU KARANTA: Akpabio: Zakka ce mu ka ga ba APC - Inji Jam'iyyar PDP

Shugaban R-APC Buba Galadima ya samu lafiya bayan yayi hadarin mota
Yadda motar Buba Galadima tayi kaca-kaca bayan yayi hadari

A lokacin da tsohon ‘Dan siyasar yayi hadari, wasu sun zata abin sai ya fi haka muni ganin yadda motar ta sa kirar SUV tayi kaca-kaca. Wannan hadari ya aukowa Buba Galadima ne bayan ya dawo daga wata ta’aziyya da ye je a Jihar Yobe.

Injiniya Buba Galadima wanda shi ne tsohon Sakataren Jam’iyyar CPC na kasa yana tare da ‘Dan sa mai suna Sadiq Galadima da wani ‘Dan uwan sa Muhammad Galadima da wasu 'Yan uwan sa mutum 2 duk a lokacin da wannan musiba ta faru.

Ko da dai Galadima bai fito yayi wata magana bayan da yayi hadarin ba, an ga hotunan sa cikin koshin lafiya bayan ya dawo asibiti. Bayan aukuwar abin, an dai ga wasu su na murnar ibtila'in da ya aukawa ‘Dan adawar na Shugaba Buhari.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng