An kashe mutane 3 a rikici tsakanin makiyaya da yan kasuwar awaki a Adamawa

An kashe mutane 3 a rikici tsakanin makiyaya da yan kasuwar awaki a Adamawa

Akalla mutane uku ne suka mutu a sakamakon wata rikici da ta balle tsakanin wasu Fulani makiyaya da dillalai yan kasuwar awaki dake jihar Adamawa, kamar yadda jaridar Sahara Reporters ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito baya ga kisan mutane uku, an samu da dama da suka samu munanan rauni a sanadiyyar wannan rikici da ya faru a kasuwar dabbo ta Ngurore.

KU KARANTA: Babu abin da ka tabuka game da cigabanmu – Matasan jihar Sakkwato ga Tambuwal

Majiyarmu ta tattauna da wani shaidan gani da ido mai suna Mohammed Bala, sai dai ya bayyana mata cewa ba shi da masaniya game da hakikanin musabbabin da ya kunna wannan rikici.

An kashe mutane 3 a rikici tsakanin makiyaya da yan kasuwar awaki a Adamawa
Kasuwar awaki

Amma Bala ya tabbatar da cewa shi da idanunsa ya ga gawarwaki har guda uku kwance cikin jini, inda ya kara da cewa shima da kyar da sudin goshi ya tsallake rijiya da baya.

Sai dai da majiyarmu ta tuntubi Kaakakin rundunar Yansandan jihar, Othman Abubakar, sai yace ba zai iya tabbatar da faruwar lamarin ko akasin haka ba, saboda yana kan hanyarsa ta zuwa aikin Hajji a Saudiya.

Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

ko a http://twitter.com/naijcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng