Saurayi ya kar ubansa sannan ya kashe kansa da wuqa, kaico!
- Wani mutum mai shekaru 32 a duniya ya soke mahaifin shi da wuka
- Lekan ya kashe mahaifin shi, inda daga baya ya halaka kanshi har lahira
- Yayan shi dai yace yana da tabin hankali
Wani mutumi mai suna Lekan Adediran, Dan shekaru 32 a duniya ya soke mahaifin shi Lawrence mai shekaru 80 a duniya, inda daga baya ya kashe kanshi.
Lekan dai ance yana da tabin hankali, ya kashe mahaifin shi a ranar litinin a Efon Alaaye, shelkwatar karamar hukumar Efon dake jihar Ekiti.
Ofishin dillancin labarai ya ruwaito cewa hukumar yan sandan yankin sun tabbatar da faruwar al'amarin, inda suka ce an fara bincike.
Ganau ba jiyau ba sunce Lekan ya kashe kanshi da fasassar kwalbar da ya soke mahaifin shi da ita.
DUBA WANNAN: Komawar Akpabio APC ta dawo mana da duk asarar mu ga PDP
Babban yayan wanda yayi ta'asar, Ojo Adediran, ya kai rahoton ofishin yan sandan yankin Efron, yace dai kanin nashi bashi da cikakken hankali, kari da cewa ya aikata laifin ne gurin karfe 9:45 na dare.
Jami'in hulda da jama'a na yan sandan jihar Ekiti, Caleb Ikechukwu yace gawarwakin suna ajiye a gurin aje gawarwakin babban asibitin Efon Alaaye.
"Dan uwan Lekan ne ya tunkare mu da al'amarin, ya sanar damu yanda kanin shi ya halaka mahaifin su kuma ya halaka kanshi. Gawarwakin su a yanzu haka suna babban asibitin Efon domin gano sanadiyyar mutuwar su. Duk da haka yan sanda sun kokarta gurin kwantar da hankulan jama'a da suka tashi.
"Ba zamu dogara da wani labari da aka kawo mana ba, zamuyi bincike da kanmu don tabbatar da ingancin labarin." inji Caleb.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng