Kotu ta gindayawa Saraki Katanga tsakanin sa da Lauyan kolu da Sufeto Janar na 'Yan sanda
Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, wata babbar kotu dake zamanta a garin Jabi na babban birnin tarayya na Abuja, ta sanya hijabi tare da katanga ta kare shugaban majalisar dattawa, Abubakar Bukola Saraki.
Alkalin kotun M. A Nasir, shine ya yanke wannan hukuncin da yammacin yau Laraba da yake tsawatar da lauyan kotun, Abubakar Malami da sufeto Janar na 'yan sanda, Ibrahim K. Idris akan su dakatar da muzgunawa Saraki.
Rahotanni sun bayyana cewa, sau da dama sufeto janar na 'yan sanda na gayyato Saraki domin titsiye tare da tsare shi dangane da wasu laifuka da ake zargin sa da aikatawa musamman tuhumar sa da laifin fashi da makamin da ya auku a garin Offa na jihar Kwara.
KARANTA KUMA: Osinbajo ya gana da Gwamnan jihar Kebbi a fadar Aso Villa
Sai dai a sakamakon korafi mai lamba CV/2454/18 da wasu lauyoyi goma masu kare hakkin dan Adam suka shigar, kotun ta yanke wannan hukunci ne mai bayar da garkuwa ga shugaban na majalisar dattawa.
Lauyoyin da sanadin jagorancin Barrister Ikenga Imo Ugochinyere, sun nemi kotun akan ta yi nazari cikin tanadin sassa na 34, 35, 36, da 41 cikin kundin tsari dake jaddada kare hakkin dan Adam cikin kasar nan.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:
https://facebook.com/naijcomhausa
https://twitter.com/naijcomhausa
Asali: Legit.ng