Hotunan ‘Yan Majalisan PDP su na shakatawa da ruwan kwalba a gaban su

Hotunan ‘Yan Majalisan PDP su na shakatawa da ruwan kwalba a gaban su

An hangi wasu ‘Yan Majalisar Tarayyar Najeriya da ke karkashin lemar Jam'iyyar PDP a cikin Majalisar kasar su na shakatawa bayan takkadamar da ta faru jiya inda DSS su ka zagaye harabar Majalisar.

Hotunan ‘Yan Majalisan PDP su na shakatawa da ruwan kwalba a gaban su
An hangi wasu 'Yan Majalisa jiya tare da kayan maye a gaban su

Mun samu hotunan wasu daga cikin ‘Yan Majalisar Wakilan Tarayya rike da kayan barasa bayan an yi rikici a Majalisar tsakanin ‘Yan Majalisa da kuma Jami’an tsaro na DSS masu farararen kaya a jiya Talata da safe.

Jami’an DSS sun yi kokarin hana ‘Yan Majalisar shiga ofisoshin su wanda har ta kai Mukaddashin Shugaban Kasa Yemi Osinbajo ya tsige Shugaban na DSS. Gwamnati ta kuma yi alkawarin daukar matakin da ya dace.

KU KARANTA: Wani Sanatan PDP ya bayyana shirin da Jam’iyyar APC ta ke kullawa a Majalisa

Bayan duk an gama wannan rikici ne ‘Yan Majalisar su ka samu kutsawa cikin Majalisar inda aka hange su a zaune su na hutawa dauke da kwalaben giya. Wani ‘Dan Jaridar nan ta Punch ne ya dauki hoton ‘Yan Majalisar a jiyan.

Wata daga cikin Hadiman Shugaban kasa Buhari watau Lauretta Onochie tayi magana game da wannan abu inda tace hakan ya nuna cewa ‘Yan Majalisar adawa ne su ka shirya abin su ka shirya jiya don neman magana.

‘Yan Majalisar Wakilan da Sanatocin Jam'iyyar PDP sun yi ikirarin cewa ‘Yan Majalisan da ke tare da Shugaba Buhari ne ke kokarin tsige Bukola Saraki. Sai dai kuma kusan babu wani Sanatan APC da aka gani a Majalisar jiya.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng