Bidiyon Sanata Dino Melaye ya na saida gyada a kai ya jawo magana

Bidiyon Sanata Dino Melaye ya na saida gyada a kai ya jawo magana

Mun samu labari cewa wani bidiyo da aka ga ‘Dan Majalisar da ke wakiltar Yankin Kogi ta Yamma a Majalisar Dattawa watau Dino Melaye ya na saida gyada a kan sa ya ba jama’a mamaki.

Bidiyon Sanata Dino Melaye ya na saida gyada a kai ya jawo magana
Sanata Dino Melaye lokacin da yake tallar gyada

An hangi Sanata Dino Melaye wanda ba bakon jawo magana bane yana tallar dafaffiyar gyada daure a saman kan sa. Wasu sun yi wuf sun dauki Senata Melaye hoto lokacin da yake wannan talla a kan titi dauke da kwano.

Ana tunani wannan abu ya faru ne tun a bara, sai dai yanzu ne hankalin mutane ya karkata zuwa bidiyon. ‘Dan Majalisar ya kuwa yi ciniki inda jama’a da dama su ka tsaya su ka saye gyadar domin katse yawun marmari.

KU KARANTA: Abin da ya sa na bar Jam'iyyar APC - Abdulfatahi Ahmed

Wata Baiwar Allah ta nemi Sanatan ya rage mata farashin gyadar inda ya nuna cewa fau-fau ba zai yi rangwame ba domin farashin kaya sun tashi a zamanin Shugaba Buhari. ‘Dan Majalisar yana cikin ‘Yan adawar Gwamnatin nan.

An ji Sanata Melaye yana cewa ba zai saida gwagwani 3 na gyadan a Naira 100 ba. ‘Dan Majalisar yace yana saida kowane gwangwani a kan kudi Naira 50 har yayi ‘yar shagube ga Shugaba Buhari mai kokarin yaki da barna a kasar.

Kun san cewa Sanata Ben Bruce ya bayyana shirin da APC ta ke yi a Majalisa. Ben Murray Bruce ya kuma bayyana cewa su na magana da kasashen waje domin ganin Gwamnatin Shugaba Buhari ba ta yi wa Majalisa katsalandan ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng