Arewa gida: Wasu 'yan Arewa 3 sun nuna bajinta a Nahiyar Afrika

Arewa gida: Wasu 'yan Arewa 3 sun nuna bajinta a Nahiyar Afrika

Wasu daliban jami'a masu nazarin ilimin na'ura mai kwakwalwa watau Computer Sceince a Turance daga Arewacin Najeriya sun baje kolin fasahar su tare kuma da yin zarra a nahiyar Afrika ta dalilin wata manhajar wayar salula da suka kirkira.

Daliban dai da suka hada da Fatima Auwal Aliyu, da Peter Balarabe, da Salisu Yusuf Bako dukkanin su daga jami'o'i biyu na Arewacin Najeriya na Jami'ar Abuja da kuma Jami'ar Ahmadu Bello ta Zariya sune suka yi hadin gwuiwa wajen kirkirar fasahar.

Arewa gida: Wasu 'yan Arewa 3 sun nuna bajinta a Nahiyar Afrika

Arewa gida: Wasu 'yan Arewa 3 sun nuna bajinta a Nahiyar Afrika

KU KARANTA: Mummunan hatsari ya rutsa da dan majalisa daga jihar Filato

Legit.ng dai ta samu cewa wannan manhaja dai za ta yi aiki ne a kan waya komai-da-ruwanka mai amfani da tsarin Android ko iOS.

Manhajar dai kamar yadda muka samu, mutum zai iya amfani da ita a wayarsa ta salula ya kunna abubuwan da ke cikin gidansa, kamar su fanka, talabijin, soket da dai sauran su.

Wannan manhaja da wadannan dalibai suka kirkiro ce dai ta zo ta hudu a karshen gasar da aka gudanar kuma yanzu haka suna aiki tare da kungiyar Startup Arewa don ganin an samu masu zuba jari an yawaita na'urar da manhajar saboda mutane su amfana.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel