Gwamnatin Tarayya ta salwantar da $1m wajen yaso 'Yan Najeriya daga 'Kasar Rasha

Gwamnatin Tarayya ta salwantar da $1m wajen yaso 'Yan Najeriya daga 'Kasar Rasha

Mun samu rahoton cewa, gwamnatin tarayya ta bayyana adadin kudade da ta salwantar wajen yaso 'yan Najeriya 355 dake cikin hali na tagayyara da ƙaƙa nika yi daga kasar Rasha bayan an kammala gasar ƙwallon ƙafa ta kofin duniya na 2018.

Ministan harkokin kasashen ketare, Mista Geofferey Onyeama, shine ya bayyana wannan rahoto yayin ganawa da manema labarai cikin birnin Abuja a ranar Litinin din da ta gabata, inda ya ce an yaso 'yan Najeriya har kaso biyu daban-daban.

Mista Geofferey yake cewa, gwamnatin ta salwanatar da zunzurutun kudi na kimanin Dalar Amurka Miliyan daya wajen yaso 'yan Najeriya 155 da kuma 200 a kaso daban-daban.

Ya ci gaba da cewa, gwamnatin ta yaso kaso na biyu na 'yan Najeriya 200 tare da wasu 'yan kasar Ghana 17 da suka gaza dawowa kasar su bayan halartar gasar kwallon kafa ta kofin duniya a kasar Rasha.

Gwamnatin Tarayya ta salwantar da $1m wajen yaso 'Yan Najeriya daga 'Kasar Rasha

Gwamnatin Tarayya ta salwantar da $1m wajen yaso 'Yan Najeriya daga 'Kasar Rasha

Kamar yadda shafin jaridar The Nation ya bayyana, gwamnatin kasar Ghana da sanadin Ministan ta na harkokin kasashen ketare, Shirley Botchway, ta yabawa Najeriya dangane da wannan abun son barka da ta yiwa al'umma kasar ta.

KARANTA KUMA: Wadanda suka sauya sheƙa sai sun yi nadama, 'Yan Najeriya na tare da APC - Wamakko

Legit.ng ta fahimci cewa, gwamnatin Najeriya ta yaso al'ummar ta ne yayin da suka afka cikin halin na tagayyara sakamakon gazawa ta dawowa kasar su bayan halartar gasar kwallon kafa ta kofin duniya a kasar Rasha.

Onyeama ya kuma bayyana cewa, a sakamakon umarni na shugaban kasa Muhammadu Buhari a a gare sa tare da Ministan Sufuri na jiragen sama, Hadi Srika, ya sanya suka gaggauta yaso 'yan mutanen daga kasar Rasha zuwa nan gida Najeriya.

Kazalika wannan shi yake bayyana yadda gwamnatin shugaba Buhari ta tsunduma cikin kare martabar al'ummar ta ko ina suke a fadin duniya.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko buƙatar bamu labari, tuntuɓe mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku leƙa shafukanmu na dandalin sada zumunta a:

https://facebook.com/naijcomhausa

https://twitter.com/naijcomhausa

Source: Hausa.legit.ng

Mailfire view pixel