Shegiyar uwa: Yadda wata mata ta yi karyar sace ta da ‘yarta don damfari mijinta miliyan N15m

Shegiyar uwa: Yadda wata mata ta yi karyar sace ta da ‘yarta don damfari mijinta miliyan N15m

-Jami'an tsaro sun yi nasar damke matar da ta hada baki da wasu don karbar kudi a wajen mijinta

- Sai dai hakar ta bai cimma ruwa ba sakamakon bankado maboyarsu da 'yan sanda suka yi

Rundunar ‘yan sanda ta kasa reshen jihar Legas sun kama wata mata mai suna Hadijat Kabiru mai kimanin shekaru 45 a duniya, bisa laifin zargin ta da boye ‘yar ta domin neman kudin fansa a gurin mijinta mai suna Muraino Kabiru.

Shegiyar uwa: Yadda wata mata ta yi karyar sace ta da ‘yarta don ta damfari mijinta miliyan N15m

Shegiyar uwa: Yadda wata mata ta yi karyar sace ta da ‘yarta don ta damfari mijinta miliyan N15m

Tun da farko dai rahotanni sun bayyana cewa Muraino ya samu kiran waya a ranar 2 ga watan Agustan nan daga wasu mutane da suka bayyana kan su a matsayin masu garkuwa da mutane, inda suka bayyana masa cewa matarsa Hadijat da kuma ‘yarsa Hamidat mai kimanin shekaru 18 sun yi garkuwa da su akan hanyarsu ta zuwa Asibitin masu tabin hankali dake yankin Oshodi a jihar Lagos.

Masu garkuwar sun bukaci da ya bayar da kudin fansa kimanin Naira miliyan 15 domin a sako masa iyalinsa, sannan suka umarce shi akan kada ya yi yunkurin sanarwa da ‘yan sanda domin kubutar da su.

Kwamishinan ‘yan sandan na jihar Legas Imohimi ya bayyana cewa wannan lamarin Hadijat ce ta kitsa shi domin damfarar mijinta.

KU KARANTA: Wannan rayuwa: Tsananin talauci ya sanya wata kaka ta siyar da jikarta

“A ranar Alhamis ne wani mutum mai suna Alhaji Muraino Kabiru mazaunin titin gwamna dake yankin Ikotun ya kai rahoto Ofishin ‘yan sanda dake Ikotun cewar matarsa tare da 'yarsa an yi garkuwa da su a lokacin da su ke kan hanyar zuwa asibitin masu tabin hankali dake Oshodi" In Ji Imohimi.

Ya kara da cewa sun bukaci da in ba su Naira miliyan 15 domin su sakomin iyali na. Jin haka ya sa na tura jami'an ‘yan sanda masu yaki da garkuwa da mutane domin ganin sun yi nasarar damke wadannan mutanen".

“Binciken jami'anmu a karon farko ya gano cewa wadannan mutanen suna boye ne a yankin Ado-Odo Ota da ke jihar Ogun, inda suka garzaya can domin ganin sun yi nasarar damke su".

“Bayan sun je yankin ne suka yi nasarar kama wani matashi dan kimanin shekaru 29 mai suna Ahmed Kudus, tare da matarsa Hadijat Rufai, amma sai dai ragowar sun arce. Ba tare da bata lokaci ba Hadijat ta bayyana cewa ta hada baki ne da wadannan mutanen domin damfarar mijinta" Kwamishinan ‘yan sandan ya tabbatar.

Latsawannandominsamunsabuwarmanhajarlabarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmunadandalinsadazumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idankuna da watashawarakobukatarbamulabari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Hausa.legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel