Masu ba Gwamnan Kano shawara sun bi sahun tsohon Mataimakin Gwamna sun yi murabus

Masu ba Gwamnan Kano shawara sun bi sahun tsohon Mataimakin Gwamna sun yi murabus

Mun samu labari cewa an sake samun wasu da su ka ajiye aikin su da Gwamnatin Jihar Kano. Wasu daga cikin masu ba Gwamna Umar Ganduje shawara ne su kayi murabus daga matsayin su.

Masu ba Gwamnan Kano shawara sun bi sahun tsohon Mataimakin Gwamna sun yi murabus
Wasu kusoshi a wajen Gwamnan Kano sun yi murabus

Yakubu Alhajiji Nagoda wanda kawo yanzu yake ba Gwamna Umar Abdullahi Ganduje shawara game da harkokin da su ka shafi makabartu ya ajiye aikin na sa. Alhajiji Nagoda ya aikawa Mai Girma Gwamnan takarda yana mai sanar da shi hakan.

Bayan nan kuma akwai Abdulhadi Zubairu Chula wanda ke ba Gwamnan Jihar shawara kan sha’anin Kungiyoyin kasashen waje da Kungiyoyi masu zaman kan-su. Shi ma Hadimin Gwamnan yayi godiya na damar da aka ba sa yayi wa Kano hidima.

KU KARANTA: Mutanen da za a iya nadawa Mataimakin Gwamna a Kano

Ban da Dr. Abdulhadi Zubairu Chula, mun ji labari cewa wani Hadimin Gwamnan mai suna Shamsu Kura wanda ake yi wa lakabi da Wakilin Talakawa ya bar mukamin sa. Duk cikin su dai babu wanda ya bayyana dalilin barin sa ofis a wasikun.

Sauyin shekar da ake samu a Jihar Kano bai rasa nasaba da barin tsohon Gwamnan Jihar Kano Rabi’u Musa Kwankwaso APC. Jiya ne ma Mataimakin Gwamna Farfesa Hafiz Abubakar ya bar kujerar sa inda yace ba zai iya aiki da Gwamna Ganduje ba.

Mun samu labari cewa tsohon Kwamishinan Jihar Kano kuma 'Dan takarar Sanata a Yankin Kano ta Kudu watau Abdullahi Sani Rogo ya nada Malam Bashir Aminu mai magana da yawun sa.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa

Ko a http://twitter.com/naijcomhausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng