Ikon Allah: wata dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure, hotuna

Ikon Allah: wata dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure, hotuna

- Wata mata ta samu karuwar haihuwa a lokacin da ta cika shekaru 60 a duniya

- Matar ta samu juna biyu ne a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aure

- majiyar Legit.ng ta sanar da ita cewar matar ta samu haife diyar ta mace cikin koshin lafiya

Wata mata, Grace Arowojolu, ta samu haihuwa a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aurenta. Matar ta haifi diyar ta mace cikin koshin lafiya.

Legit.ng ta ci karo da wannan labari ne a shafin sada zumunta na Facebook na Funmi Akeju, wata 'yar uwa ga Arowojolu.

Ikon Allah: wata dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure, hotuna
Dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure

Akeju ta rubuta, "jama'a ku taya ni yiwa ubangiji godiyar nuna ikonsa a kan 'yar uwa ta mai shekaru 60 a duniya da ta samu haihuwa a karo na farko bayan shekaru 30 da yin aure.

Daga cikin mutanen da suka tabbatar da labarin haihuwar Arowojolu akwai Ogundare Modupe Christy wacce ta kasance daya daga cikin ma'aikatan asibiti da suka karbi haihuwar dattijuwa Arowojolu.

DUBA WANNAN: Matar shugaban kasar Gambiya ta yiwa matan Najeriya da suka haihu goma ta arziki, hotuna

Ajama tayi addu'ar neman karin lafiya ga mai jego da kuma diyar ta.

Labarin haihuwar na Arowojolu ya matukar bawa jama'a mamaki, musamman idan aka yi la'akari da yawan shekarunta na haihuwa.

Masana harkar lafiya da likitoci sun sha bayyana cewar yana da matukar wuya ga matar da ta wuce shekaru 50 a duniya ta dauki ciki balle ma ta kai ga haihuwa.

Ikon Allah: wata dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure, hotuna
Wata dattijuwa mai shekaru 60 ta haihu bayan shekaru 30 da aure

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa

Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng

Tags: